Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya ruwaito cewa an gabatar da jerin tattaunawa kan Mahdawiyya mai taken “Zuwa ga Al’umma Mai Manufa”, da nufin yaɗa koyarwa da ma’arifa masu alaƙa da Imam Mahdi (Allah Ya gaggauta bayyanarsa), ga ma'abota ilimi da kuma masu sha’awar wannan fanni.
Dangane da bayanan da suka gabata, gaibar Imam Mahdi (A.S.) abu ne da ya zama dole. Sai dai tun da dukkan matakan da shugabanninmu masu girma suka ɗauka suna da nufin ƙarfafa imani da aqidar mutane, akwai fargabar cewa gaibar hujjar Allah ta ƙarshe za ta iya haifar da babbar illa ga addinin Musulunci. Saboda haka, an fara wannan gaiba ne da tsari mai kyau da kuma shirye‑shirye na musamman.
Tun shekaru da dama kafin haihuwar Imam na goma sha biyu (A.S.), an riga an yi magana a kan fakuwarsa da dalilin faruwarta, kuma wannan magana ta zama sananniya a majalisun Ahlul‑Bayt (A.S.) da sahabbansu. Haka kuma, yadda Imam Hadi da Imam Askari (A.S.) ke hulɗa da mabiyansu ya sauya zuwa wata sabuwar hanya, inda hulɗar ta zama takaitacciya. A hankali mabiyan Ahlul‑Bayt suka fahimci cewa ba lallai ba ne su kai ziyara ga Imam kai tsaye domin warware dukkan bukatunsu na addini ko na rayuwa ba; suna iya komawa ga wakilai da amintattun mutane da Imamai suka naɗa domin su taimaka musu.
Bayan shahadar Imam Hassan al‑Askari (A.S.) da fara fakuwar Imam Hujjat ibn al‑Hasan (A.S.), dangantaka tsakanin Imam da al’umma ba ta yanke gaba ɗaya ba. Mutane suna hulɗa da Imam ta hanyar wakilansa na musamman, kuma ta hannunsu suke karɓar saƙonnin Imam da amsoshin tambayoyinsu. A wasu lokuta ma wasu daga cikin mabiyan suna samun damar ganawa da Imam ta hanyar waɗannan wakilai. A wannan lokaci ne Shi’a suka saba da komawa ga malamai domin sanin nauyin addininsu a lokacin da Imam yake a boye.
Gaibar ɗan gajeren lokaci (Ghaybat al‑Sughra)
Bayan shahadar Imam Hassan al‑Askari (A.S.) a shekara ta 260 bayan hijira, Imancin Imam na goma sha biyu ya fara, kuma daga wannan lokaci aka fara boyuwarsa (gaiba) ta farko wadda ake kira “Ghaybat al‑Sughra”. Wannan lokaci ya ci gaba har zuwa shekara ta 329 bayan hijira, kusan shekaru 70.
Babban abin da ya bambanta wannan lokaci shi ne cewa mutane suna hulɗa da Imam Mahdi (A.S.) ta hanyar wakilai na musamman. Ta hannunsu suke karɓar saƙonnin Imam da kuma amsoshin tambayoyinsu.
Wadannan wakilai na musamman, waɗanda dukkansu manyan malamai ne kuma zababbun Imam Mahdi (A.S.), su ne guda huɗu kamar haka:
1. Uthman bin Sa’id al‑Amri – shi ne wakili na farko bayan fara gaibar Imam, kuma ya rasu a shekara ta 267 bayan hijira. Tun kafin haka ma wakili ne ga Imam Hadi da Imam Askari (A.S.).
2. Muhammad bin Uthman al‑Amri – ɗan wakili na farko ne. Bayan rasuwar mahaifinsa ya karɓi wannan matsayi, kuma ya rasu a shekara ta 305 bayan hijira.
3. Hussain bin Ruh al‑Naubakhti – ya yi wakilci na tsawon shekaru 21, sannan ya rasu a shekara ta 326 bayan hijira.
4. Ali bin Muhammad al‑Samuri – shi ne wakili na ƙarshe, kuma ya rasu a shekara ta 329 bayan hijira. Da rasuwarsa ne ƙaramar gaiba ta ƙare.
Dukkan waɗannan wakilai Imam Hassan al‑Askari (A.S.) da Imam Mahdi (A.S.) ne suka zaɓa suka kuma gabatar wa mutane. A lokacin gaibar farko, kowane wakili kafin rasuwarsa yana sanar da mutane wakili na gaba wanda Imam Mahdi (A.S.) ya zaɓa.
Dangantaka da waɗannan wakilai da kuma samun damar wasu daga cikin Shi’a su kai ziyara ga Imam dinsu a lokacin wannan boyuwa ya taimaka matuƙa wajen tabbatar da haihuwar Imami na goma sha biyu. Wannan ya faru ne a lokacin da makiya ke ƙoƙarin sa mutane su yi shakka game da haihuwar ɗa ga Imam Hassan al‑Askari (A.S.). Haka kuma wannan lokaci ya zama shiri mai kyau domin fara babba gaiba
Doguwar gaiba (Ghaybat al‑Kubra)
A kwanakin ƙarshe na rayuwar wakili na huɗu, wani wasiƙa daga Imam Mahdi (A.S.) ta zo masa inda aka ce:
«بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمنِ الرَّحِیمِ یَا عَلِیَّ بْنَ مُحَمَّدٍ السَّمُرِیَّ أَعْظَمَ اللَّهُ أَجْرَ إِخْوَانِکَ فِیکَ فَإِنَّکَ مَیِّتٌ مَا بَیْنَکَ وَ بَیْنَ سِتَّةِ أَیَّامٍ فَاجْمَعْ أَمْرَکَ وَ لَا تُوصِ إِلَی أَحَدٍ فَیَقُومَ مَقَامَکَ بَعْدَ وَفَاتِکَ فَقَدْ وَقَعَتِ الْغَیْبَةُ التَّامَّةُ فَلَا ظُهُورَ إِلَّا بَعْدَ إِذْنِ اللَّهِ تَعَالَی ذِکْرُهُ وَ ذَلِکَ بَعْدَ طُولِ الْأَمَدِ وَ قَسْوَةِ الْقُلُوبِ وَ امْتِلَاءِ الْأَرْضِ جَوْراً... .» (الغیبه، شیخ طوسی، ج ۱، ص ۳۹۵)
“Da sunan Allah Mai rahama Mai jin kai. Ya Ali bin Muhammad al‑Samuri! Allah Ya ƙara wa ‘yan’uwanka lada saboda musibar rasuwarka. Domin kai za ka rasu cikin kwanaki shida. Don haka ka shirya al’amuranka, kuma kada ka naɗa wani a matsayin magajinka bayan rasuwarka; domin cikakkiyar boyuwa (Gaiba) ta fara. Ba za a ga bayyanata ba sai bayan izinin Allah, kuma hakan zai kasance bayan wani lokaci mai tsawo, lokacin da zukata za su yi tsauri kuma duniya za ta cika da zalunci.” (Alghaiba, Sheikh Tusy, j:1, s:395)
Saboda haka, da rasuwar wakili na ƙarshe a shekara ta 329 bayan hijira, aka fara doguwar gaiba wanda ake kira “Ghaybat al‑Kubra”. Wannan lokaci yana ci gaba har zuwa ranar da Allah Ya so, lokacin da gajimaren boyuwa za su kau, duniya kuma ta amfana da hasken jagorancin Imam Mahdi (A.S.). Insha Allah.
Wannan tattaunawa za ta ci gaba...
An samo daga littafin “Negin‑e Afarinesh”, tare da ɗan gyara kadan
Ra'ayinka